Labaran yau da kullum

Labarin wani Ɗan Jahar Katsina da ya kafa tarihi a Jami’ar ABU Zaria

Ɗalibin nan da sunan shi yayi tashe ƴan kwanakkin ga a yanar gizo, Dr. Sale Murtala Dandashire, ya bayyana cewa yana daga sirrukan nasarorin shi jajircewa, himma da dagewa ga maida hankali ga karatun shi. Sannan ya shawarci dukkan ɗalibai da su ɗauki wannan a matsayin makami a fafutukar su ta neman ilimi a duk makarantun da sun ka tsinci kansu. Dakta Dandashire ɗan garin Ketare a karamar hukumar Kankara dake cikin Jahar Katsina ya kafa tarihi a Jami’ar ABU Zaria inda ya lashe kambunan yabo guda goma sha-ukku (13) a bikin kammala karatu da makarantar karatun likitanci (ABU Medical School) ta gudanar na shekarar bana 2019. Ɗalibin ya zama gwarzo a darussa kamar haka:
1. Best in Physiology
2. Best in Surgery
3. Best in Haematology
4. Best in Anatomy
5. Best in Histopathology
6. Best in Project (Community
Medicine)
7. Best in Biochemistry
8. Best in Chemical Pathology
9. Best in Pathology
10, Best in Med. Micro
11. Best in Commed
12. Best in Pharmacology
13. Best Graduating Student

Labarin gwarzon Dalibin ya dauki hankulan mutane matuƙa a kafofin sada zumunta; Twitter da Facebook, ganin cewa gurbin karatun likitanci (Medicine course) abu ne ba mai sauki ba. Ƙarawa d ƙarau, mun samu labarin cewa wanga ba shi bane karo na farko da Jami’ar ABU Zaria take yaye dalibai likitoci da sunka yi zarra a kasar, shekarar bara 2018 ma, sun yaye wata daliba macce mai suna Dakta Aisha Humairah Abaji yar asalin Jahar Nasarawa da ta samu kambunan yabo guda tara (9). Bana an samu namiji wanda ya doke ta da kambu guda hudu (4).

Tsangayar karatun likitanci ta Jami’ar ABU, wato Ahmadu Bello Univesity Medical School, Zaria tace nasarar Dakta Dandashire ba tashi bace shi kadai, ta kasa ce baki daya, musamman yankin Arewa da ma Gwamnatin Jahar Katsina.

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

WhatsApp Join Group