Gargajiya da Tabi'u

Salon siyasar da akeyi a Jahar Sakkwato na tursasa masu Sarautun gargajiya babban koma baya

Sarauta a Jahar Sakkwato ta kasance abu mai tarihin da kab fadin Nijeriya babu irinta wanda duk wani tarihi na kasar Hausa yakan fara tanan kasancewar a wancan zamani Sakkwato ta kasance mahada ga Daular Gobirawa da kuma Sarakunan Daular Usmaniyya amman sai gashi a halin yanzu wadannan masarautu sun fara kasancewa abun dariya ta dalilin koma bayan da yan siyasa ke janyowa, inda a halin yanzu da yawa daga cikin manyan yan siyasa sunada nasu zabin sarakuna wanda yanzu har takai ga yawancin sarakuna doli sai sun fito hili sun bayyana dan takarar da sukeso domin tsira da kujerunsu inda dayawa daga cikin sarakuna suna ji suna gani yan siyasa ke tsige su da karfi da yaji suna nada wanda suke so.

Yanzu haka a masarautu da yawa sarakunan dake mulki ba’a ko nadasu ba wanda kuma a al’ada duk sarautar da za’ayi sai kaga anyi taro anyi kade-kade da bushe-bushen al’ada don taya sabon sarki murna wanda yanzu haka da yawa daga cikin sarakuna ba’a ganinsu da kima don ana ganin kamar su ma siyasa ce ta aza su ba cancanta ba.

Gyara kayanka…

Hassan Haruna Gobir

Hassan Haruna Gobir, from Sabon Birni in Sokoto State, is GobirMob.com publisher and writer. He primarily focused on Nigeran politics, Gobir News and Sports.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

WhatsApp Join Group