Kundin Tarihi

Tarihin Daɗaɗɗar Daular Gobir da jerin sunayen Biranenta

Tarihin Gobir ya faro tun shekaru dubu biyar (5,000) da tashi ko hijira na tsawon shekara dubu daya da dari daya (1,100). Ta bakin bayanin Shugaban “Maradi Institute for Social Sciences” IRSH, Malam Sani Habou Magagi, In muka dauki tarihi tun daga zamansu a Gabas ta tsakkiya, Gobirawa sun taso daga Baghdada. Kenan kasar Iraki ta yanzu, wanda daga can ne suka taso. Mazamninsu na biyu ko birni shine Birnin Kudus a Jerusalem tsakanin Kasar Palasdinu da Isra’ila, Birninsu na ukku shine Birnin Gubur a Yamen inda suka samo sunan “Gobir”, Na hudu shine Birnin Karbala cikin Saudi Arabiya, Na biyar shine Birnin Masar (Egypt cikin Afrika). Birni na shidda kuma shine Birnin Surukal cikin Tunisiya, Na bakwai shine Birnin Tunasse shima duk cikin Tunisiya (Afrika-ta-Arewa), Birni na takwas shine Birnin Bagazam (wanda yanzu yake cikin Jahar Agadez) a Jamhoriyar Niger, Afrika-ta-Yamma. Na tara kuma shine Birnin Aigadasse shima cikin Jamhoriyar Nijar, Na goma shine Birnin Tinliguilit a Nijar shima, Na sha-daya shine Birnin Marandat a Nijar, Na sha-biyu shine Birnin Toro a cikin Nijar, Na sha-ukku shine Birnin Lalle cikin Nijar, Na sha-hudu shine Birnin Gwararrame cikin Nijar. Sai na sha-biyar Birnin Alkalawa cikin Nijeriya a Jahar Sakkwato, Birni na sha-shidda shine Birnin Dakwarawa cikin Jamhoriyar Nijar, Na sha-bakwai shine Birnin Gawon-gazau cikin Nijeriya.

Birni na sha-takwas shine Birnin Maradi cikin Jamhoriyar Nijar (Da Djibon Taouba ya biya ya sada zumunci da danginsu Katsinawa) sannan sai na sha-tara kuma na karshe wato Birnin Tsibirin Gobir a Nijar. Kenan biranen su sha-tara ne, daga Iraqi zuwa Nijar, cikin hijra ko kaura ta tsawon shekara dubu daya da dari daya (1,100); Kuma cikin waɗannan tsawo hijirorin, Gobirawa na farko sun yi auratayya da wasu ƙabilun da sunka tarar a tafiyar tasu.

Shugaban na IRSH ya kara da cewa, Birnin Tsibiri an kafashi ne a cikin ƙarni na 19, wato a shekarar 1835, Djibon Taouba ya sara Tsibirin Gobir; Gobirawa sun kafa birnin a shekarar 1835, bayan yaƙin Dakwarawa, tsakanin Sultan Muhammadu Bello (Sarkin Sakkwato na biyu bayan Usman Danfodio ubanshi) da Sarakuna biyu: daya na Katsinar Maradi, mai suna Sarki Raouda da gudan na Tsibiri wanda ake cema Sarki Ali.

Ta bakin Sani Habou Magagi, In munka ɗauki cikin jerin Sarakunan Gobir su dari ukku da tamanin (380), kamo daga Sarki na farko zuwa na yanzu, Sultan El hadj Abdourahmane Balla Marafa, zamu iya cewa Daular Gobir ta yi gagarumin tashe a lokacin zamanin Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo. Jarumtakarshi ta kai bango hudu na duniya. Cikin zamani nai babu wani mai wata ƙeta sannan kuma shine uba ga Gobirawa. Ya roƙi Allah ya bashi mu’uzija da babu irinta wadda ita ta sa ya zama sanannen jarumi har waje ga Gobir a zamanin. Abubuwanda suka jawo ci baya ga Masarautu ko Daulolin Afrika sune “Jahadi” na El Hadj Omar a Sudan ta Yamma, sai na Usmanu Danfodio a Tsakkiyar Sudan, da “Jahadi” na Mahadi a Sudan ta Gabas. Kuma cikin wannan lokacin ne, ƙarni na 19, aka yi waɗannan Jahadodin su ukku. Maganar abubuwanda suka jawo ci baya ga Dadaddar Daular Gobir, akwai Yakin Fulani na Usman Danfodio wanda ya tadda rikici tsakanin Sarkin Gobir Yunfa da yan uwanshi; Akwai kuma yaƙe-yaƙe na ƙabilanci tsakankanin wasu Masarautun Hausa, sai kuma a farkon ƙarni na ashirin 20 sanda turawan mulkin mallaka suka kunno kai a Afrika wanda ya ƙara taimakawa ga raunana waɗannan Gawurtattun Masarautu na Afrika.

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

WhatsApp Join Group