Kundin Jarumai

Tarihin Margyayiya Hajiya Binta Kofar Soro wadda ta rigya mu gidan gaskiya

Jiya, 4 ga watan Mayu, Masana’antar Kannywood ta tsaya tsit yayinda take jimamin mutuwar ɗaya daga fitattun jarumanta mata, Hajiya Binta Kofar Soro, wadda ta rigya mu gidan gaskiya sanadiyyar ƴar gajerar rashin lafiya (ance cikon ƙafa) a gidanta dake cikin Birnin Kano. Abokan sana’arta sun sanarda rasuwar jarumar wanda an ka yi bisarta a Kanon dabo a matsayin jaharta ta biyu inda take gudanarda harkokinta na kasuwanci da sana’ar Hausa film, amman asalinta daga Jahar Katsina take, mahaifarta kuma inda ta yi aurenta na farin.


Kaman Ɗiyan Margyayiya Hajiya Binta mata su guda ukku.

Kwanakki kaɗan bayan rasuwarta Margyayiyar ta yi wani jawabi mai jan hankali a kundinta na kafar sada zumunta inda take neman gafarar mabiyanta da abokan aikinta na Kannywood tana mai cewa “Ina neman gafararku. Allah ya gafarta muna gaba daya.”

Jikokin Hajiya Binta Kofar Soro Ƴantawaye Maza.

Cikakken sunanta Hajiya Binta Kofar Soro ko Hajiya Binta a taƙaice, kamar yanda abokan sana’arta a Kannywood ke yawan kiranta. An haifeta ranar 24 ga wata Nuwamba a shekarar 1970 cikin garin Katsina. In kun ka lissafa kenan yau ta nada shekaru arba’in da tara (49) kenan. Ta yi karatunta na allo da na boko duk a garinsu Katsina kamin daga bisani ta yi aurenta na farko.

Margyayiya Hajiya Binta tareda Jikanyarta.

Ta nada ɗiya tareda mijinta na farin kamin rabuwarsu. Watannin baya ma ta yi shagalin bikin auren ɗaya daga cikin ɗiyanta mata wanda mutane da dama sun ka yi dandazo dan taya ta murna.

Kaman Auren Ɗiyarta inda take tareda Angonta.

Fitattar jarumar tana yawan fitowa a matsayin uwa a Faifayen shirin Kannywood, matsayin da ya wuce gaban wasan kwaikwayo, har a zahiri ƴan wasan su na ɗaukarta tamkar uwarsu saboda rikon gaskiya, tausayi, shawarar da take basu kamar ita ta haifesu. Hajiya ƴar siyasace ta sahun gaba wadda take gwagwarmayar ƙwato ma tallakawan yankinta yancinsu da ake danne musu, yar kasuwace ita, sannan sai sana’ar da mun ka san ta da ita wato wasan kwaikwayo wadda a cikinta ta yi fice wanda shike. Tana ɗaukar matsayin uwa a faifayen shirin da take fitowa, kwatamkwacin su Hajara Usman, Saratu Daso.

Margyayiya Hajiya Binta tareda Ɗiyarta wadda suke da kama.

Hajiya Binta tana ɗaya daga cikin jerin ƴan wasan kwaikwayo ƴan asalin Jahar Katsina. Jarumai ta jima tana haskaka akwatunan kallonku. Kafar GobirMob.com na taya ɗaukacin Masana’antar Kannywood da Katsina jimamin rasuwar Hajiya Binta Kofa Soro. Muna rokon Allah ya gafarta mata, ya sa kwanciya hutu ce.

Ragowar Kamannan Jikokin Margyayiya Hajiya Binta Kofar Soro da Ɗiyanta:

DanZubair

I am Abdul-Raheem Zubair by name, Founder- Operator at GobirMob.com. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

WhatsApp Join Group